Mata na daɗa samun muƙamai a kotunan Najeriya
November 23, 2012A ci gaba da kokarin sa na neman mafita a cikin rikicin da ya yi aure ya kuma kama hanyar tarewa a cikin sashen shari'ar Tarayyar Najeriya, an rantsar da shugaba ta uku cikin tsawon watanni 15 ga kotun daukaka karar kasar dake zanman ta biyu mafi girma a tsarin shari'ar kasar.
Hankali dai ya tashi a kusan daukacin kasar ta Najeriya a lokacin da alkali na biyu mafi girman iko ya kalli na farko a ido ya zarge shi da kokarin son rai a wani ƙarin girman da ya samu ya zuwa kotun koli.
Mai shari'a Isa Ayo Salami dai yace akai kasuwa game da batun zuwansa kotun kolin da a wancan lokaci babban alkalin kasar mai sharia Alosius Katsina Alu ya bukace shi da yi. Abun kuma da ya kai ga bude sabon babi ya kuma kai ga fito fili tsohon karatun cin hancin da ake ta'allakawa da sashen shari'ar kasar ta Najeriya.
An dai share tsawon watttani har 15 ana kai kawo, an kuma kai ga nadin akalla shugabanni biyu ga kotun daukaka karar kasar dake zaman ta biyu mafi girma kuma ke cikin tsakiyar rikicin.
Ta baya baya dai na zaman mai sharia Zainab Adamu Bulkachuwa da aka kai ga rantsarwa a yau da kuma ke zaman shugaba ta uku cikin tsawon lokaci.
Mace ta farko da zata ja ragamar kotun dai mai sharia Bulkachuwa na da jan aikin sake dawo da kima da martabar sashen shari'a, da yanzu haka ke cikin rudani
Babban kalubale a gaban sabuwar shugabar dai a cewar Barrister Waziri Mamman dake zaman wani lauya mai zaman kansa dai, shine tunkarar matsalar cin hancin a matakai daban daban na kotun.
To sai dai koma ta ina take shirin farawa dai ana hasashen da kamar wuya ga sabuwar alkaliyar ta kai ga iya kawo sauyin da ake fatan gani a cikin kotun da ke taka muhimiyyar rawa ga batun shari'u na siyasa da kuma ake zargi da kasancewa babbar matattarar cin hancin na shari'un da suka shafi siyasa.
An dai ambato sunan ita kanta sabuwar alkaliyar a cikin wasu daga cikin shari'un da masharhanta ke ganin da sauran gyara a cikinsu, abun kuma da a cewar Mallam Garba Umar dake zaman masanin harkokin zamantakewar kasar ya sa da wuyar gaske a kai tudun mun tsirar shari'ar da yan kasar ke fatan gani a yanzu.
Akwai dai masu kallon sabon sauyin a matsayin kama hanyar kawo karshen fatan tsohon shugaban kotun mai shari'a Isa Ayo Salami na sake ɗana kujerar shugaban kotun, duk da cewar dai har ya zuwa yanzu ba ta kai ga karewa a cikin shari'ar da ake tafkawa ba.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman