1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata sun nuna adawa da fyade a taron "Golden Globes Award"

Yusuf Bala Nayaya MNA
January 8, 2018

Matan da suka yi fice wajen bayyana a fina-finai sun fito cikin bakaken kaya a wajen bada lambar girman don nuna goyon baya ga 'yan uwansu mata da suka fiskanci tozartawa ko ma yi musu fyade a masana'antun fim.

https://p.dw.com/p/2qTuT
Golden Globes 2018 Greta Gerwig
Hoto: picture-alliance/AP/NBC/P. Drinkwater

Bikin bada lambar girma ga fina-finan wasannin kwaikwayo da suka yi fice a duniya na birnin Los Angeles na jihar California a Amirka "Golden Globes Award" da aka yi a otel din Baverly Hilton karo na 75, ya gamu da nuna fushi na mata 'yan fim da 'yan fafutika da suka bayyana cikin bakaken kaya don nuna irin takaicinsu ga yadda mata ke fiskantar tozartawa ko cin zarafinsu daga bangaren maza a masana'antun shirya fina-finai.

Matan da suka yi fice wajen bayyana a fina-finai dai sun fito cikin bakaken kayan ne don nuna goyon baya ga 'yan uwansu mata da suka fiskanci irin wannan tozartawa ko ma yi musu fyade a masana'antun na shirya fina-finan a bikin da ke zuwa tun bayan takaddamar me shirya fina-finai Harvey Weinstein da mata da dama suka bayyana shi da aikata musu ba daidai ba.

Merly Streep 'yar wasan kwaikwayo ce:"Mun tsaya tare don jan bakin layi, abin da aka yi a lokutan baya ba zamu lamunta ba a wannan lokaci."

A yayin bikin bada lambar girman ga fina-finan a bana dai fim din "In the Fade" wanda daraktansa ya fito daga Jamus Fatih Akin ya samu lambar yabo ta fim da ya yi fice na harshen kasashen ketare.