Mata 'yan siyasa da 'yan kasuwa: Wadannan sun zama masu fada a ji a Afirka
Mata tara da suka yi fice a duniyar da maza ke kaka-gida inda suka kutsa cikin siyasa da kasuwanci da harkokin rayuwa. Hotunan sun nuna irin rawar da suka taka da inda suke.
Shugabar kasa mace ta farko da aka zaba a Afirka
Ellen Johnson Sirleaf ita ce mace ta farko da aka zaba karkashin dimukuradiyya don shugabantar wata kasa a Afirka. Daga 2006 zuwa 2018 ta zama shugabar Laberiya. Jagora ce a yaki da rashin aiki da kokarin rage basuka da yaki da Ebola. Ta sami lambar yabo ta zaman lafiya dalilin yaki a kare hakkin mata da tsaronsu. Yanzu tana jagorantar babban zauren Majalisar Dinkin Duniya kan 'yan gudun hijira.
Babban mataki ga mata a Habasha
Sahle-Work Zewde ta kasance shugabar kasar Habasha mace ta farko tun daga watan Oktoba, karfin iko dai na a hannun firaminista da majalisar ministocinsa; matsayin Zewde ana kwatanta shi da na shugaban kasar Jamus, sai dai duk da haka zaben nata ya yi fice a inda maza ke da wuka da nama kan harkokin kasuwanci da siyasa. Majalisar ministocin Habasha rabi mata ne.
Babbar mai fada a ji ga Faransawa
Tsohuwar ministar harkokin wajen Ruwanda Louise Mushikiwabo za ta zama babbar sakatariya a kungiyar kasashe masu magana da harshen Faransanci a 2019. Duk da kasancewar kasarta ana magana da harshen Ingilishi kan harkokin aiki da tattalin arziki da ilimi fiye da shekaru 10, zaben nata na zama abin alfahari a ci gaban diflomasiya. Ta samu yabo ciki har da na shugaban kasar Faransa.
Mace guda da kasashe 193
Wata macen mai fada aji: Amina Mohammed, mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya tun daga farkon shekarar 2017. Daga shekarar 2002 zuwa 2005. Da ma tuni ta fara aiki da MDD karkashin shirin cigaban muradin karni, daga bisani mai ba da shawara ta musamman ga babban Sakataren MDD Ban Ki-moon, shekara guda kuma a matsayin ministar muhalli a gwamnatin Muhammadu Buhari.
Jagorar yaki da basuka a Namibiya
A Namibiya, mace na jagorantar gwamnati: Tun daga watan Maris 2015, Saara Kuugongelwa-Amadhila ta kasance firaminista, mace ta farko a wannan ofis a Namibiya, a baya ta rike mukamin ministar kudi da kudiri na rage wa kasarta bashi. Masaniya a fannin tattalin arziki, ta kasance mamba a majalisar dokoki tun daga shekarar 1995.
Gimbiya mai takama da albarkatun mai sai rashin kwarjini
Isabel dos Santos tsawon lokaci ana cece-kuce a kanta a Angola. 'Ya ga tsohon shugaban kasar Angola José Eduardo dos Santos wanda ya sa ta zama darakta a kamfanin mai na kasar Angola a 2016. Amma sabon shugaban kasa na yaki da nuna alfarma ya kori Isabel dos Santos cikin aikinsa na farko bayan zargin sanya kudin kamfanin man kasar zuwa wani asusun banki a Dubai.
Mai taka rawa ta karkashin kasa
Wata da aka santa kan boye-boye da taka tsantsan ita ce Jaynet Kabila 'yan biyu ta Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. 'Yar tsohon shugaban Kwango. Jaynet Kabila ta kasance a majalisa, kuma ita ke da mallaki na gidan Talabijin da intanet da gidajen Rediyo. A shekarar 2015 mujallar Faransa ta Jeune Afrique ta bayyana ta a matsayin mace mafi karfin fada a ji a gwamnati.
Minista da ta kafa tarihi a Mali
Wata da ke zama sabuwa kan harkokin kasashen waje ita ce Kamissa Camara: Matashiya mace ta farko a matsayin ministar harkokin wajen Mali. 'Yar shekaru 35 Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da aka sake zabensa ya nada ta. Ta kasance daya daga cikin mata 11 a gwamnatinsa. Majalisar ministocin ta Mali na da ministoci 32.
Attajira a harkar mai da ke taimako
Folorunsho Alakija 'yar Najeriya mai kudin da suka kai Dala miliyan dubu daya da dari shida mai kamfanin nan na Famfa Oil mai hakar mai, ta kasance mace ta uku mafi arziki a Najeriya. An gano sunanta cikin mutane da ke da arziki a duniya kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa, kamar Isabel dos Santos. Alakija na da gidauniya da ke tallafa wa marayu da zawarawa.