1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Shirye-shiryen rantsar da Biden

January 20, 2021

Ana ci gaba da tsaurara matakan tsaro a biranen Amirka dabam-dabam, musamman Washington DC babban birnin kasar, inda za a rantsar da sabon shugaba mai jiran gado Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris.

https://p.dw.com/p/3o8bq
USA Biden Einweihungsprobe
Jami'an tsaro jibge a birnin Washington DC, domin gudun abin da kaje-ya-zoHoto: J. Scott Applewhite/AP Photo/picture alliance

Rahotanni sun nunar da cewa, sojojin tsaron cikin kasar da aka jibge a birnin na Washington sun zarta adadin wadanda Amirkan take da su yanzu haka a Iraqi. Jibge wadannan jami'an tsaron da  suka hadar da 'yan sanda gami da sauran jami'an tsaron farin kaya dai, ba ya rasa nasaba da barazanar da 'yan ta'adda kyankyasar cikin gida suka yi na cewa za su kara kawo farmaki makamancin wanda suka kai a ginin majalisar dokoki makwanni biyu da suka gabata. 

Karin Bayani: Sabon kudirin neman tsige Shugaba Donald Trump

An toshe dukkan manyan hanyoyi da gadoji na shiga Washington, an kuma yi shingaye a farfajiyar ginin majalisa da fadar shugaban kasa da sauran gine-ginen gwamnati, yayin da masu kantuna suka toshe tagogi da kofofinsu tituna kuma kusan sun yi wayam in ban da sojoji da 'yan sanda da ke muzurai cikin damarar yaki, suna bayar da hannu ga wadanda fita ta zama dole gare su.
Karajin motocin yaki da jiragen sama tuni suka zama jiki cikin 'yan kwanakin nan a yawancin jihohi, a wani mataki na tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro, biyo bayan mamaye majalisar dokokin Amirkan da magoya bayan Trump suka yi. Ko bayan mutane kusan 130 da ya zuwa yanzu aka damke dangane da harin da aka kai a majalisar, hukumar binciken manyan laifuka ta kasar FBI, tana ci gaba da bin diddigin kafofi dabam-dabam na dakile dukkan wasu matsalolin tsaro.

Cartoon USA Das Drama Trump
Trump ya yi ta tayar da kura kan sakamakon zaben shugaban kasa

Karin Bayani: Trump ya ce shi yai nasara

Ko da a ranar Lahadin da ta gabata ma, sai da aka kama wani Bature mai suna Richard Barnet da bindiga da daruruwan harsasai a birnin Washington DC, amma daga bisani aka sake shi. Tuni dai shugabar gudanarwar birnin Washington Madam Mauren Bauza ta bukaci jama'a su yi hakuri su kalli bikin rantsar da sabon shugaban kasar ta akwatunan talabijin dinsu daga gida, a dai-dai wannan lokacin da ta tabbatar da cewa, shugaba mai barin gado Donald Trump zai fice daga birnin tun kafin a rantsar da Joe Biden.