1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin ƙungiyar EU a kan Jamus

September 8, 2006
https://p.dw.com/p/BukC

Kungiyar Tarayyar Turai ba zata dauki wani mataki akan Jamus dangane da gibin kasafin kudin kasar ba, kamar yadda aka ji daga bakin piraministan kasar Luxemburg Jean-Pierre Juncker mai shugabanci gamayyar kasashen dake amfani da takardun kudi na Euro. Wannan bayanin na nuna gamsuwar kungiyar ce akan yadda Jamus ke bakin kokarinta wajen daidaita al’amuran kasafin kudinta. A Brussels jami’an kungiyar sun yi madalla da bayanin da ministan kudin Jamus Peer Steinbrück ya bayar a game da cewar gibin kasafin kudin kasar ba zai zarce kashi 2 da digo 8 cikin dari a wannan shekarar ba, wanda zai yi daidai da sharuddan kungiyar na kashi 3 cikin dari ga kasashe masu amfani da takardun kudin Euro.