1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin Amurka a Afrika ta Tsakiya

Reed, JaredDecember 28, 2012

Amurka ta kwashe jami'ian ofishin jakadancinta daga jamhuriyar Afrika ta Tsakiya bayan da 'yan tawaye ke cigaba da mamaye yankuna a arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/17ACb
Residents of Central African Republic participate in a marching protest along the streets of the capital Bangui, December 21, 2012. Hundreds of people protested outside the French Embassy in Central African Republic on Wednesday, throwing stones at the building and tearing down the French flag in anger at a rebel advance in the north of the country. Picture taken December 21, 2012. REUTERS/Stringer (CENTRAL AFRICAN REPUBLIC - Tags: SOCIETY CIVIL UNREST POLITICS CRIME LAW)
Zentralafrikanische Republik - Proteste in BanguiHoto: Reuters

Amurkan ta ce daukar wannan matakin ba wai ya na nufin lalalcewar dangantaka da Jamhuriyar ta Afrika ta Tsakiya ba ne, wani yunkuri ne in ji Amurkan na kare al'ummarta da ke kasar a saboda haka ne ma ta gargardi Amurkawa da su gujewa shiga kasar a dan tsaknin nan saboda abubuwa da ka je su komo.

Ita ma dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce kwashe wasu daga cikin jami'anta daga Jamhuriyar ta Afrika ta Tsakiya saboda halin da ta tsinci kanta a ciki.

Tuni dai shugaban kasar Francois Bozize ya yi kira ga Amurka da Faransa da su agaza masa wajen dakile 'yan tawayen wanda yanzu haka ke kokari danna kai babban birnin kasar domin karbe iko da shi, sai dai Faransa ta ce ba za ta bada wani agaji na soja ba.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammed Awal Balarabe