1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin Jamus da Brazil kan satar bayanai

October 26, 2013

Jamus da Brazil sun ce za su gabatar da wani ƙuduri a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya wanda zai nemi kawo ƙarshen satar bayanai na sirri da Amirka ke yi.

https://p.dw.com/p/1A6aB
Hoto: picture-alliance/dpa

Wani jakada a zauren na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya so manema labarai su sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewar yana ganin wannan ƙudiri da za a gabatar zai samu karɓuwa sosai saboda babu ƙasar da ke son a rika tatsar bayananta.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da ake tsaka da dambarwa tsakanin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Amirka saboda zargin Amirkan da ta yi na sauraron wayoyin da Merkel ɗin ke bugawa, inda Merkel ɗin ta ce dole ne Amirka ta dakatar da wannan ɗabi'a daga nan zuwa ƙarshen wannan shekarar.Ita ma dai Faransa wannan matsayi ta ɗauka inda ta koka dangane da sauraren wayoyin wasu mutane a ƙasar da jami'an leƙen asirin Amirkan suka yi.

A watan da ya gabata ma dai shugabar Brazil Dilma Rouseff ta gabatar da ƙorafi gaban babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya dangane da zargin Amirka na keta mata haddi da saɓawa dokar ƙasa da ƙasa wajen karanta sakonninta batun da ya sanya Rouseff ɗin fasa yin wata ziyara da a baya ta shirya kai wa Amirka.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane