1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin 'yan gudun hijira na Tarayyar Turai

Umaru AliyuJune 8, 2016

Hukumar kungiyar hadin kan Turai ta ce za ta bukaci ganin yarjejeniyar da za ta dace da kowace kasa a jerin kasashen da 'yan gudun hijiran suka fi fito.

https://p.dw.com/p/1J2WS
Symbolbild Menschenhandel in der EU
Hoto: picture alliance/dpa/PAO/Mittelmeer

Mukaddashin shugaban hukumar, Frans Timmermann yace da farko hukumar za ta nemi cimma yarjejeniya da Jordan da Lebanon, sai kuma kasashen Jamhuriyar Nijar, da Najeriya, da Senegal, da Mali, da kuma Habasha, tare da kara karfafa hadin kan da ke akwai tare da kasashen Libiya da Tunisiya.

Karkashin wannan shiri, kungiyar hadin kan Turai za ta tanadi taimakon kudi ga kasashen da suka amince domin hadin kai da ita, misali ta hanyar yaki da kungiyoyi masu fataucin jama'a zuwa Turai, tare da kuma karbar 'yan gudun hijiran da suka koma kasashen su na asali, bayan an ki amincewa da bukatunsu na mafakar siyasa a Turai. Kungiyar ta ce za ta kuma tanadi hukunci da zai hana taimako ga duk kasar da ta ki ba da hadin kan kan batun na yan gudun hijira.

Äthiopien Federica Mogherini beim EU Afrika Gipfel
Hoto: DW/G. Tedla

Bugu da kari kuma, kungiyar hadink an Turai zata karfafa batun shigowar baki yan ci rani ta hanyoyi na halaliya, misali, kwararru daga ketare. Kwamishiniyar harkokin waje ta kungiyar hadin kan Turai, Federica Mogherini ta ce mataki ya zama wajibi.

Mukaddashin shugaban hukumar kungiyar Frans Timmermann ya ce daga yanzu zuwa shekara ta 2020, hukumar za ta ware abin da ya kai Euro miliyan dubu takwas domin kasashen masu tasowa da suka amince da hadin kai da kungiyar hadin kan Turai kan batun na 'yan gudun hijira. Idan kuma aka sami goyon baya daga masu zuba jari masu zaman kansu da sauran kasashen Turai, taimakon yana iya kai wa misalin Euro miliyan dubu 31.

Deutschland Hannover Ankunft Syrischer Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Hollemann

Wakilan majalisar Turai sun nuna ra'ayoyi daban-daban game da wannan kudiri na hukumar. Wakilan manyan jam'iyyu sun yi marhabin da shirin, amma sun bayyana shakku game da yiwuwar samun jarin da kungiyar take bukata dokin taimakawa kasashen masu tasowa. Manfred Weber, shugaban yan jam'iyyar masu ra'ayin yan zaman jiya a majalisar ya yi tsokaci da cear a watan Nuwamba na bara, lokaxcin taro a Malta, an amince da kafa wani asusu na taimakon nahiyar Afika, amma ya zuwa yanzu, kasashe 28 na kungiyar hadin kan Turai abin da suka tara bai wuce Euro miliyan 81.7 ba, daga adadin Euro miliyan dubu daya da dari takwas da suka yi alkawari.