1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matan Najeriya na tona asirin masu fyade

November 5, 2019

A Najeriya, ana samun karuwar mata da ke fitowa fili su bayyana yadda aka yi musu fyade a baya. Ko da a kwanakin baya sai da matar wani fitaccen mawaki ta zargi wani fitaccen pasto da yi mata fyade tun tana 'yar karama

https://p.dw.com/p/3SUQY
Nigeria Met Too Kaduna
Hoto: DW/K. Gänsler

 

Mata na taron gangami tsakanin wadanda suka fusata kan yadda matsalar fyade ke kara yawa a unguwanninsu a Lagos. Wata da aka ci zarafinta ta hanyar fyade a Najeriya ta ce sun daina yin shiru kan batun. Yanzu dai da yawa daga cikinsu na fitowa fili su bayyana sunan wadanda suka yi musu fyade a baya.

Soniya Obi Okodo ta ce tun tana 'yar shekara biyar a duniya kawunta ya sha yi mata fyade, inda ta ce hakan ya sanya ta cikin yanayi na damuwa da dimuwa.Ta ce "  Ko barci ba na iya yi saboda abin da ya faru da ni a baya, na kan ji ni tamkar ina wani waje da nake a shekaru 10 da suka gabata, ina tsaye ina kallon abin da ke faruwa da ni."

Nigeria Met Too Kaduna
Shugabannin kungiyoyin mata na sauraran wadanda aka yi wa fyade a KadunaHoto: DW/K. Gänsler

 Soniya ta ce rashin kwatar mata hakkinta lokacin da aka yi mata fyade, ya taimaka wajen sanya ta cikin halin da ta shiga. Ta ce a yanzu ta zabi ta bude cikinta ta bayyana komai tana mai cewa: "Daya daga cikin dalilan da suka sanya nake jina wani iri shi ne, ina ganin ba a yi min adalci ba, saboda ba wai ya yi min fyade ne kawai a gidan mahaifina ba, a'a, ya yi min fyade ne a dakin mahaifiyarsa. Yana yi min fyade a gidanmu da ke Lagos da kuma kauye idan muka je hutu.

Wata mai fafutukar kare hakkin mata da ke kokarin kwantar wa da wadanda aka ci zarafinsu hanakali, Tobore Ovore ta ce idan wadanda aka ci wa zarafi suna fitowa su yi magana, zai kusanta su da adalcin da suke fatan samu. Ta ce: Zan iya cewa an kawo karshen al'adar yin shuru idan an yi wa yarinya fyade. A yanzu wasu matan na fitowa suna magana, hakan abu ne mai kyau. Ina goyan bayan hakan. Al'adar yin shurun na hana masu fafutukar kwato musu hakki da kuma masu kokarin kwanar musu da hankali domin su dawo su ci gaba da rayuwa kamar kowa."

Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
'Yan sanda na taimakawa wajen kamo masu fyade a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Bala Elkana mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Lagos ya ce an yi gyara a kan dokar hukunta masu yin fyade, wanda hakan ne ya taimaka wajen bai wa matan kwarin gwiwar fitowa su bayyana wanda yai musu fyaden domin a yi musu adalci.