1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matar Mugabe na son zama shugabar Zimbabuwe

Suleiman Babayo/Lina HoffmannOctober 28, 2014

Grace Mugabe na so ta gaji kujerar mulkin Zimbabuwe bayan da aka zabeta shugabar mata ta ZANU-PF da ke mulki. Sai dai tana fuskantar kalubale daga Joice Mujuru.

https://p.dw.com/p/1DdJL
Grace Mugabe
Hoto: picture-alliance/dpa

Yayin da a babban taron jam'iyyar ta ZANU-PF na watan Disamba za a tabbatar da Grace Mugabe a matsayin shugabar mata ta jam'iyyar, abin da zai tabbatar da shigarta cikin lamuran siyasa, uwargidan shugaban na jaddada cewa tun da al'ummar kasar na kaunarta dole ta tsaya a dama da ita a harkokin siyasar Zimbabuwe.

Simbabwe Wahlen 31.07.2013 Mugabe
Hoto: Reuters

"Duk kuna bukatar na tsaya takara domin zama shugabar kasa, mai zai hana haka? Ni ba 'yar Zimbabuwe ba ce?"

A matsayinta na mamba a kwamitin koli na jam'iyyar, kuma tsohuwar sakatariyar shugaban, za ta taka mahimmiyar rawa wajen neman gadon kujerar mijinta, Robert Mugabe wanda yake mulkin Zimbabuwe tun shekarar 1980, lokacin da kasar ta samu 'yanci daga kasar Birtaniya. Mugabe dan shekaru 90 da haihuwa ya auri wannan mata da ya girma da kimanin shekaru 40.

Wilf Mbanga editan wata jaridar kasar ta Zimbabuwe da ake bugawa a Internet ya soki Grace Mugabe kan yukurin gadon mulki daga mijinta:

Simbabwe Wahlen Robert Mugabe in Mahuwe
Hoto: AP

"Grace ba 'yar siyasa ba ce. Grace ba ta da wani sani a kan harkokin siyasa. Grace ba ta da kwarewa bisa abin da ya shafi jam'iyyar ZANU-PF ko harkokin siyasa baki daya."

Wilf Mbanga ya ce a fayyace take Shugaba Mugabe yana goyon bayan matarsa ta gaji kujerar mulkin kasar, domin kare dukiyar da suka tara. A shekara ta 2018 za a sake gudanar da zaben shugaban kasar.

Tuni aka fara samun baraka a cikin jam'iyyar ZANU-FP mai mulki, inda Grace Mugabe da magoya bayanta suka zargi mataimakiyar shugabar kasar Joice Mujuru da neman samun madafun iko ta hanyar da ta saba ka'ida.