1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasan jihar Filato a Najeriya sun yi kira ga zaman lafiya.

Abdulaye MaidawaMarch 16, 2015

Matasan Musulmi da Kirista a jihar Filato ta Tarayyar Najeriya, sunsha alwashin cewa, ba zasu bari 'yan siyasa su yi amfani dasu ba don tada hankula a lokacin babban zabe da kuma bayan sa.

https://p.dw.com/p/1ErXt
Hoto: DW/Katrin Gänsler

A baya dai, ba kasafai matasan suke haduwa cikin dandali guda ba, sakamakon iri-irin matsalolin tashe-tashen hankullan da suka gudana a baya a wannan jiha. Magoya bayan dan takarar zaben shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyar APC a Tarayyar ta Najeriya Janar Mohammadu Buhari ne suka shirya taron, inda dimbin jama'a mabiya addinin Kirista da Musulmi suka hallara da nufin ganin cewar jama'ar Filato sun cigaba da zaman lafiya kamar yadda yanzu haka jihar ke cin moriyar zaman lumana da juna.

Matasa sun fara fahimtar minene Demokradiyya.

Kafin yanzu dai ba kasafai mabiya addinan kan shiga unguwanin juna ba, mussaman ma a birnin na Jos, to sai dai yanzu da alamu matasa sun fahimci cewar sun gaji da tura mota wa 'yan siyasa suna bulesu da hayakin motar. Don haka a wannan zabe a cewarsu, zasu hada kai da juna, kuma zancen tashin hankali na siyasa, banda su a bana.

nigeria entführung schülerinnen proteste frauen boko haram
Hoto: reuters

Babu batun tashin hankali a harkokin zabe.

Kasancewar yanzu lokaci ne na siyasa, masharhanta na ganin ya kamata matasa a sassa daban-daban na Najeriya su yi koyi da wadannan matasa na jihar Filato wajen shirya tarurukan fadakar da matasa 'yan uwansu hanyoyin zaman lafiya da fahimtar juna a wannan lokaci da ake gab da yin zabe, maimakon sa hannu a takarda na neman gujewa tarzoma a lokacin zaben da kuma bayan sa wanda kuma akasari ba tare da yin biyayya ga abubuwan da aka sanya hannun a kansu ba.