1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

HdM: Matashi mai raba audugar mata

December 29, 2021

Idris Bilyaminu mai shekara  21 mai karatun digiri a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, yana dinka audugar mata ya raba wa matasa a kyauta. Yana ma koyar da yanda ake dinka ta.

https://p.dw.com/p/44xMm
Damenbinde
Hoto: AAMIR QURESHI/AFP/Getty Images

Yana da abokan gudanar da wannan aiki sama da 15. Ya ce ganin yadda da dama daga cikin wasu matasa mata ba su da kudin sayen audugar, shi ya sa ya ga akwai bukatar wannan tallafi. Kan batun nagartarta da kuma tsafta, ya bayyana cewa ana iya amfani da ita sau biyu ko uku domin sukan yi amfani da sabon tawul ne da kuma atamfa wajen yin audugar. Audugar ba ta da illa ga mace ko kadan.

Ganin mawuyacin halin da wasu  Mata da ‘Yammata Matasa ke ciki na kasa sayen  audugar mata ta sanya matashin fara tunanin hanyar da za a samu sauki wajen samar da audugar da za a iya amfani da ita sau biyu ko zuwa uku. A cikin shekara ta 2020 ne shi da ‘yan tawagar tasa suka kirkiri wani shiri na tallafin bayar da audugar mata wanda  suka sanyawa suna "Ceto Yara Mata''.

Matashin ya ce tabbas akwai kalubale domin sun sha wahalhalu wajen koya wa wasu mata musamman kafin a yarda da su, a gefe guda suna kuma samun hauhawar farashin kayan aiki.

Babbar nasarar da suka samu ita ce koya wa mata sama da 500 yadda ake dinka audugar a cikin watanni uku. Sun kuma samu karbuwa a wurin al'uma. Babban burinsa bai wuci samun damar da za su mallaki yadda za su iya samar da audugar mai yawa ba domin tallafa wa mata musamman ‘yan gudun hijira. A karshe ya jawo hankalin Matasa wajen yin abin da al'umma za su amfana da su.