1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai sana'ar gidajen kifi na zamani a Najeriya

December 19, 2018

Wani matashi da ke jihar Sakkwato Abdul-ra’uf Mansur wanda kuma ya kammala digirinsa a jami’a ya rungumi sana’ar gidajen kifi na zamani a gidajen masu hannu da shuni wato Aquarium a turance.

https://p.dw.com/p/3ANlf
DW Reportage über Plastikverbrauch in Chile | Fische in Aquarium
Hoto: DW/N. Messer

Shi dai wannan matashi mai cikakken suna Abdul-rauf Mansur Babangida dama dai tuni ya kammala digirinsa a fannin kiwon kifi a jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato, ya ce ya yanke shawarar rungumar harakar kifin ne gadan-gadan sakamakon rashin aikin yi da ya tsinci kansa a ciki. Yanzu haka dai wannan matashi ya kawo wani sabon abu da bakasafai aka saba ganinsa ba a birnin na Sakkwato na samar da nau’ukan kifi kama daga na  kallo da kuma mai cin dattin kafa. Ko da yake bayan shafe tsawon shekaru matashin na gudanar da wannan sana’a, da sanadin hakan ya kai shi ga bude kamfani  mallakarsa, mai suna  DR. Fish Spa Aquarium. Duba ga yadda matashin ta kaishi ga bude rassa na wannan kamfani a wasu sassan biranen kasar.