1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai sana'ar kiwon kaji a Najeriya

January 4, 2017

Adam Muhammad Abdullahi wanda ake kira da sunan Adamu Yaro ya sami nasarar samar da injin kyankyasar kwai na kaji da sauransu a Abuja.

https://p.dw.com/p/2VFCE
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Ossinger

Shi dai Adam Muhammad Abdullahi wanda sam ba shi da wata alaka da bangaren fasahar kere- kere ya fara nazarin yadda zai samar da injin kyankyasar kwai ne tun a shekara ta 2013 sakamakon irin yadda yake matikar son samun wadanda za su kyakyashe masa kwayayansa, sabili da sha'awar kiwon da yake da shi.A kowace rana injn da ya kera ya kan iya yin aikin kyankyasar kwai sama da dari biyu ko ma fiye da haka.