1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashin da ya kirkiri wasannin Bidiyo

Abdullahi Tanko Bala
September 26, 2018

Mamman Sani Usaini matashi ne da ya kamala karatunsa na jami'a kuma ya mayar da hankali wajen samar da irin wasannin da ake yi a wayar salula ko wanda ake hadawa da akwatunan talabijin wato Video Games.

https://p.dw.com/p/35XDA
Olympische Sommerspiele 2012 in London Zuschauer mit Handy
Hoto: Reuters

Mamman Sani Usaini dan shekaru 26 da haihuwa na zama matashi na farko a Nijar da ya rungumi aikin nazari da fasahohin kimiyya ta hanyar zane zanen hotuna na barkwanci tun yana dan matsakaicin shekaru.

Sai dai  matashin ya fi kauna da sha’awar kayan wasan yara na zamani da akan iya jonawa a akwatin talabijin ko kuma a wayoyin hannu na salula. Ta wannan hikimar ce ma ya kirkiro wasan da ya sanyawa suna Jaruman Sahel inda ya rika yada al’adun Nijar da yankin Sahel baki daya.

A Irin nasarorin da ya samu Usaini yace da wannan sana’a yake ci da sha da taimakawa iyalai da dangi da kuma sauran al’umma. Ya samar da shirye shirye da dama da suka hada da wadanda ake iya samu a wayar salula.

Batun kalubale kuwa Mamman Sani Usaini yace musamman samun kayan aikin da yake bukata na daga cikin matsalolin da ya fuskanta yana mai cewa duk abinda mutum zai yi idan ya sa hakuri da juriya yana iya cimma burinsa.