1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiya na tallafa wa dalibai a Zamfara

December 27, 2017

Matashiya mai shekaru 20 ta himmatu wajen ba da gudummuwa ta fuskar ilmi, inda take sayen kayan karatu tana rabawa makarantu musamman ga yayan marasa galihu.

https://p.dw.com/p/2pztv
Nigeria Makoko schwimmende Schule in Lagos
Hoto: Reuters/A. Akinleye

Farida Musa na samun kudaden ba da wannan gudummuwa ne ta hanyar sana'ar da take yi a cikin gida inda ta ce ta damu da irin yadda ta ga dalibai ke cikin yanayin rashin samun ingantaccen karatu.

"Wasu akwai wadanda kila iyayen su ba su da karfin da za'a ce sun tanadar musu wadannan kayan karatu, to ina tunanin hanyar da nabi zai sa su amfana da shi an rage matsala ko kuma rashin abun karatu na wurin yaran nan" 

Nigeria Kano Mädchen Nijab
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Matashiyar ta ce ta samu karfin gwiwar ba da ta ta gudummuwa ne bayan da ta ga girmar matsalar ta shafukan sada zumunta, 

"Akwai hotuna ko in ce posting na Facebook da naga wasu daga cikin al'ummar Jihar Zamfara suna ta yi dangane da irin matsalolin da ake fuskanta ta bangaren karatu. Za ka ga wadansu makarantun babu kayan karatu misali irin su kayan makaranta ko kuma litattafai da sauran su. Wannan ya sa naga zan iya iya taimakawa."

Wasu daga cikin dalibai sun bayyana yadda tallafin mtasiyar ke inganta rayuwar karatun su, wanda suke ganin ka iya taka rawar gani a nan gaba.