1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya

January 28, 2013

Oby Ezekwesili ta zargi gwamnatin Najeriya da cin hanci da rashawa fiye da ƙima

https://p.dw.com/p/17TAA
epa03046191 (FILE) A file photograph Goodluck Ebele Jonathan, President and Commander-in-Chief of the Armed Forces of the Federal Republic of Nigeria speaks during the general debate at the 66th session of the United Nations General Assembly at United Nations headquarters in New York, New York, USA, on 21 September 2011. Media reports state on 31 December 2011 that President Goodluck Jonathan has declared a state of emergency in areas affected by attacks from the Islamist group Boko Haram. Borders will be temporarily closed in the north-eastern states of Yobe and Borno, and central state of Plateau. EPA/JASON SZENES *** Local Caption *** 00000402928322 +++(c) dpa - Bildfunk+++
Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/dpa

A wani abun da ke zaman ƙoƙari na kwance zane a kasuwa ga ɓangaren gwamantin tarrayar Nijeriya dake iƙirarin neman kawo ƙarshen rashawa da cin hanci, an buɗe sabon kace na ce a tsakanin tsohuwar jam'iyar bankin duniya dake zargin gwamantin shugaba Jonathan da almubazzarancin da ya haura ƙa'ida da kuma gwamnatin da ke cewar zuƙi ta malle ce, kuma zance irin na 'yan tasha.

Ta dai buɗa baki ta kuma ambato abun da ya kai dallar Amurka milliyan dubu 67 ko kuma kasafin kuɗin ƙasar ta Najeriya na shekara biyu a matsayin almubazzarancin da tsohuwar mataimakiyar shugaban bankin duniya Oby Ekwesilezi tace gwamantocin marigayi Umar Musa 'yar Adua da kuma abokin takunsa dake ci yanzu Good luck Ebele Jonathan suka tafka yayin mulki.

To sai dai kuma daga dukkan alamu ta faɗi mai ɗaci a idanun mahukuntan na Abuja da suka ce Oby ba ta da ta ido, sannan kuma ta sha ƙarya a ƙoƙarin ta'allaka gwamantin yanzu da batun cin hanci da rashawar dake rufa masa baya.

Plakate gegen Korruption gibt es überall – doch oft sind sie wirkungslos Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 29. Oktober 2010 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Abuja, Nigeria
Hoto: DW/Katrin Gänsler

A gaba ɗaya ma dai a cewar ministan yaɗa labaran Nijeriya gwamantin ta 'Yar Adua da Jonathan ya gada daga baya ta samu gadon dallar Amurka milliyan dubu 43 ne ba 67 ba kamar yadda tsohuwar jami'ar kuma tsohuwar minista a gwamantin chief Olusegun Obasanjo ke iƙirari.

Karatu irin na gaskiya ko kuma adawar masu adawa dai , zargin jami'ar na zuwa ne dai lokacin da ƙasar ke ƙara fuskantar matsin lambar yaƙar batun cin hanci da ƙasa da ƙasa ke zargin ta da jan ƙafa a kai.

Sai fa a farkon makon nan ne aka fara jin ƙanshin yiwuwar zuwa kotu a ɓangaren wani ɗan Majalisar da ake zargi da karɓar na goro har dala 620,000 domin wanke kamfuna a badaƙalar tallafin man fetur ɗin dake zaman annoba a ƙasar.

Sannan kuma ana fuskantar tafiyar hawainiya ga su kansu kamfanonin da jami'an dake da ruwa da tsaki da batun da kuma mafi yawansu ke da alaƙa da jiga jigan jami'yar PDP mai mulkin ƙasar ta Najeriya.

Ko a babbar mashaƙatar hutawa ta Davos a ƙasar Switzland dai da ƙyar da gumin gosi shugaba Jonathan ya rinƙa ƙoƙarin fidda kansa cikin zargin cin hancin ƙasar, zargin kuma da a cikin gida 'yan adawar ƙasar suka ce gaskiya ne karatun Obi,

LAGOS, NIGERIA - JULY 15: A detail of some Nigerian Naira, NGN being counted in an exchange office on July 15, 2008 in Lagos, Nigeria. (Photo by Dan Kitwood/Getty Images)
Hoto: Getty Images

Senata Lawalli Shu'aibu dai na zaman Sakataren jami'yar adawar ƙasar ta ACN.

Abun jira a gani dai na zaman mafita ga karatun cin hancin da sannu a hankali ya kai ƙasar kuma shirin baro ta cikin rami.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Yahouza Sadisou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani