1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar karuwar yunwa a inda ake fada

June 3, 2014

Kungiyar Tallafin Abinci ta Duniya ta kashe euro miliyan 140, wajen agazawa mabukatu a sassa daban-daban na duniya da ke fama da rikici da suka hadar da Siriya.

https://p.dw.com/p/1CBSg
Welthungerhilfe Horn von Afrika Somalia
Hoto: AP

Kungiyar bada tallafin abinci ta duniya, ta bayyana damuwanta dangane da halin da al'ummar kasar Siriya ke ciki, sakamakon yakin basasa da ya rusa birane masu yawan a kasar.

A rahotanta na shekara ta 2013 a birnin Berlin kungiyar ta ce, wasu biranen na Siriya sun kasance tamkar Jamus ce bayan yakin duniya na biyu. Wannan kungiyar dai tana bayar da tallafin abinci ne a sassa daban-daban na duniya ga mabukatu ciki kuwa har da Siriya.

Shugabar kungiyar Bärbel Diekmann ta ce, zaben shugaban kasa da ke gudana, wadda kuma kasashen duniya suka yi suka akai, ba zai yi tasiri ba dangane da matsanancin halin da al'umma ke ciki, wanda kuma har yanzu da sauran rina a kaba dangane da gano bakin zaren warwareshi, tunda bangarori biyu da ke adawa da juna sun ki zama kan teburin tattaunawa.

Welthungerhilfe - Sierra Leone 2012
Hoto: Desmarowitz/Welthungerhilfe

Kungiyar Tallafin Abincin da ke da cibiyarta a nan Jamus da ke samun tallafin kudi daga hukumomi kamarsu Ma'aikatar harkokin waje ta Jamus da Kungiyar Tarayyar Turai EU, ta kashe kimanin euro miliyan 140 a shekarar ta 2013 data gabata. Inda ta bada tallafin gaggawa a kasashen Sudan ta Kudu da Siriya da kuma Philippines kamar yadda shugabar Bärbel Diekemann ta yi bayani:

"Ma'aikatanmu sun kai kayayyakin agaji a yankunan da aka fi yin kashe-kashe. Wadanda suka kasance a duk a arewacin Sudan".

Babban sakataren kungiyar Wolfgang Jamann, ya ce Siriya alal misali ta fuskanci matsaloli na matsanancin neman tallafin a shekara data gabata. A dangane da hakane tawagarsu ta agajin gaggawa a kusan kowane wata suna kan hanya. Haka kuma lamarin ya ke a wasu sassa na duniya, inda ake fuskantar karancin ma'aikata da za'a tura zuwa sassan da ke bukatar agaji, wanda ya sanya kungiyar shiga wani wadi na tsaka mai wuya wajen cimma burinta na tallafawa dukkan mabukatu. Baya ga hakan akwai matsaloli na hatsari ga ma'aikatan da ke kai ire iren wannan tallafi. Akwai batu na sace su baya ga hare-haren da ake kai musu.

Welthungerhilfe Sahel-Zone
Hoto: dapd

Matsalar dai ta fi tsananta a yankunan Afrika da ke kudu da Sahara,inda ya kasance wuri mai hatsarin gaske ga kungiyoyi masu zaman kansu. Yankin arewacin Afrika alal misali ya zame dandali ne na tsoffin sojoji da kungiyoyin mayakan sa kai da suka tsere daga Libiya da ke da alaka da al-Qaeda, inda ayyukan bayar da gaji ya kasance abu mawuyaci.

Shugabar kungiyar bada tallafin abinci Dieckmann ta ce, akwai matsaloli na isar da agajin saboda yanayin wuraren da ke fama da rikicin, inda wani lokaci sai jirage masu saukar ungulu ke iya isa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal