1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar kyama da kisan baki a Afirka ta Kudu

Zainab Mohammed AbubakarApril 23, 2015

Kasashen duniya musamman wanda abin ya shafa na cigaba da nuna takaicinsu da kyamar da ake nunawa baki a kasar, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

https://p.dw.com/p/1FDTN
Gewalt gegen Einwanderer in Johannesburg
Hoto: picture alliance/dpa/K. Ludbrook

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce ta na cigaba da sa ido da nufin ganin tsaro ya tabbata a kasar a kokarinta na ganin an kawo karshen kisan baki da ake yi a kasar.

Gwamnatin da shugaba Jacob Zuma ke jagoranta ta ce tana yin duk mai yiwuwa wajen ganin rayukan bakin da ake nunawa kyama ba su sake salwanta a kasar ba domin kuwa ta baza jami'an tsaro a lunguna da sakuna da ak samu labarin hallaka baki a kasar da ma kwasar ganima daga irin dukiyar da suke da ita.

To sai dai ga alama kasashen duniya da wannan kisa na baki ya shafa ba su gamsu da irin matakan da gwamnatin kasar ta dauka yayin da wasu ke ganin ta makaro wajen dakile wannan danye aiki. Wannan ne maya sanya wasu gudanar da jerin zanga-zanga don nunawa Afirka ta Kudun da ma duniya rashin amincewarsu da abinda ke faruwa. Tarayyar Najeriya na daga cikin kasashen da aka gudanar da irin wannan zanga-zanga.

Yanzu haka dai idanun duniya na kan mahukuntan Afirka ta Kudu da suka yi alkawarin kawar da wannan kisa na baki da ake yi yayi da 'yan aksar da sauran kasashe ke dakon kunshin jawabin da basaraken Zulu zai yi nan gaba a yau kan wannan batu, wanda a baya ake kallon wani jawabi da ya yi a matsayin kanwa uwar gami ta irin halin da aka shiga.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna

Rahotanni da Sharhuna