1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro na barazana ga aikin jarida

May 3, 2019

A Najeriya dai an ga yadda aka rika garkuwa da wasu 'yan jarida da ke aiki a cikin kasar ko ma wadanda ke aiki ga wasu kafafen na ketare. Ba a kuma sake su ba sai da aka biya miliyoyin kudade a matsayin kudin fansa.

https://p.dw.com/p/3Htf7
Nigeria Abuja Mohammadu Buhari Presse
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

A yankin arewacin Najeriya musamman jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da sauransu lamuran tabarbarewar tsaro na kawo cikas ga aikin jarida a jihohin ganin yadda ‘yan jaridar basu da damar gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali. Wannan ya sanya da dama manema labarai suka dena shiga yankunan karkara don gudanar da aikinsu.

Haussa Redaktion 50 Jahre Jubiläum
Muhammad Bello wakilin DW a fagen aiki me hadari a yankin Niger DeltaHoto: DW/Jan-Philipp Scholz

Kasancewar garkuwa da mutane ta yi yawa a kauyika da yankunan da ke zama dazuka, su kuma al'umma na tsoron tattaunawa da 'yan jarida musamman a yankunan na karkara.

An dai ga yadda aka rika kama 'yan jarida ana garkuwa da su a Najeriya, ga misali an kama dan jaridar gidan rediyon Muryar Amirka da na gidan talabijin na kasa a Najeriyar. Wasu 'yan jaridar sai da aka biya makudan kudade na fansa kafin a sake su. Wannan na zuwa baya ga kalubale da suke fuskanta a bangaren jami'an tsaro da ma na gwamnati.

Kungiyoyin 'yan fafutika dai a Najeriyar na son ganin an ba wa 'yan jaridar kariya ta yadda za su rika gudanar da aikinsu yadda ya kamata.