1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun 'yan gudun hijira da kasashen EU

Lateefa Mustapha Ja'afarNovember 13, 2015

Wata sabuwa da ta bullo tsakanin kasashen kungiyar EU da ke amfani da takardun izinin shiga kasashensu na bai daya wato Schengen.

https://p.dw.com/p/1H5HB
Kwararar 'yan gudun hijira na ci gaba da daukar hankalin EU
Kwararar 'yan gudun hijira na ci gaba da daukar hankalin EUHoto: Reuters/S. Zivulovic

Kasar Ostiriya ce dai ta sanar da cewa za ta gina wani shingen waya mai nisan sama da kilomita uku tsakaninta da kasar Solobaniya domin takaita yawan 'yan gudun hijra da bakin haure da ke biyowa ta Solobaniyan a kokarin da suke na shiga Ostiriyan. Da yawa dai daga cikin 'yan gudun hijirar da suka samu isa gabar teku da ransu bayan yin kasada da rayuwarsu ta hanyar biyo wa ta Tekun Bahar Rum na son shiga Jamus da Ostiriya ne. Wannan shinge dai da Ostiriyan ta ce za ta gina na zaman irinsa na farko da aka taba ginawa tsakanin kasashen Shengen din da ke amfani da takardun izinin shiga na bai daya.