1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar yunwa a duniya

Mohammad Nasiru AwalNovember 25, 2003
https://p.dw.com/p/BvnS

A cikin rahoton da ta bayar game da matsalar karancin abinci a duniya, hukumar samar da abinci da aikin noma ta MDD wato FAO ta ce matsalar ba wai ta karancin abinci ba ne, a´a rashin daukar nagartattun matakai ne daga shugabannin siyasa. Wani burin da MDD ta sa a gaba na rage yawan mutane da ke fama da yunwa zuwa rabinsu kafin shekara ta 2015, na kara fuskantar koma-baya, duk da cewa Allah Ya wadata duniyar nan da yawan abinci da zai ishe kowa da kowa. Baya ga matsalolin fari da kamfar ruwa, matsalolin siyasa da na tattalin arziki na daga cikin dalilan da suka jawo miliyoyin mutane ke fama da rashin abin sakawa bakin salati.
Matsalar dai na da sarkakkiyar gaske, kamar yadda wani masani a al´amuran raya kasa, Ivan Illich ya nunar. Mista Illich ya ce baya ga rashin yin wani hobasa daga kasashe masu arziki don taimakawa kasashe masu tasowa, wani abin da ke jawo matsalar yunwa shine tsarin tafiyar da harkokin ciniki na duniya, inda ake nuna rashin adalci, musamman ga kasashe masu tasowa.
Abu mafi a´ala da ya kamata a yi shine a bullo da wani sahihin shirin da zummar inganta halin rayuwar jama´a a kasashe masu tasowa, ta yadda zasu rika samun abin sakawa bakin sallati ba tare da wata matsala ba. Ba kawai daukar matakin bude kofofin kasuwannin kasashe masu ci-gaba masana´antu ga kayayyakin kasashe masu tasowa ake bukata ba, a´a muhimmin abu shine daukar sahihan matakan samarwa kasashen masu tasowa kudaden shiga, don samun karfin sayan abinci da sauran kayan masarufi. Ko shakka babu rashin isassun kudade ga mutane a kasashe masu tasowa na kawo babban cikas ga ko-wane yunkuri da za´a yi da nufin cike kasuwanni da kayan abinci. Domin babu manomin da zai nome kayan abincin da ya san a karshe zubarwa zai yi saboda babu masu saya. Saboda haka yake da muhimmanci a dauki nagartattun matakan kirkiro guraben aikin yi ga jama´a ta yadda zasu rika samun kudin sayan abinci da kansu, in ba haka ba kuwa dole su ci-gaba da dogaro da taimakon abinci daga ketare.
Ko da yake taimakon kayan abinci daga kasashe masu ci-gaban masana´antu kan taimaka a samun saukin radadin wasu bala´o´i, to amma a hannu daya suna kashe zuciyar wadanda ake ba taimakon. Yawanci taimakon kaya abincin da ake bayarwar, na rarar amfanin noma ne na kasashe masu ci-gaba. Amma ita gwamnatin tarayyar Jamus ta daina ba da irin wannan taimakon raya kasa. Abin da ta ke yi yanzu shine, tana ba da kudi ne don sayen kayan abinci a kasashen masu tasowa. Haka na taimakawa a samar da guraben aikin yi a wadannan kasashe, baya ga kudaden shiga da hakan ke samarwa jama´a. Bugu da kari wannan dabarar na taimakawa wajen yaki da matsalar yunwa fiye da rarraba rarar amfanin noma daga kasashe masu ci-gaban masana´antu.