1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar yunwa da talauci a wasu kasashen Afirka

Zainab Mohammed Abubakar
April 6, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta koka dangane da bala'in yunwa da talauci a Afirka irin wanda ba a taba ganin irinsa ba tun bayan yakin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/2aoG9
Hungerkrise in Somalien
Hoto: picture alliance/dpa/F. Abdi Warsameh/AP

Aiyukan tarzoma da yake-yake da cin hanci da karbar rashawa sun jefa miliyoyin mutane cikin barazanar yunwa. Matsalar ta fi kamari a kasashen Habasha da Somaliya da Sudan ta Kudu da kasashen da ke yankin tabkin Chadi. A yanzu haka dai kungoyin ba da tallafi na duniya na cigaba da laluben hanyoyin samun agajin da za a shawo kan wannan babban kalubale da ke fuskantar duniya.

Kawo yanzu dai abun da aka samu bai taka kara ya karya ba, musamman daga alkawura da kasashe masu cigaban masana'antu suka yi. Su ma dai kasashen Afirka a karkashin jagorancin Tarayyar Afirka a ba a barsu a baya ba wajen goyon bayansu ga wadanda wannan bala'i ya ritsa da su. Mayakan kungiyar Boko Haram dai sun dauki lokaci suna cin karensu babu babbaka a tsakanin kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi inda dubban mutane sun rasa rayukansu sannan tada kayar bayan da 'yan kungiyar ke yi ta ta'azzara matsalar yunwa.

Najeriya da ke da arzikin man fetur dai ta yi alkawarin bayar da agajin dala biliyan daya don tinkarar wannan matsala. Wannan lamari ya farantawa da dama rai saboda yadda kasashen Afirka ke tallafawa kawunasu. Ba wai Najeriya ce kawai ta taka rawa wajen bada wannan agaji ba, Yuganda ma ta baya bayar sai dai a nata bangaren ta karbi 'yan gudun hijira ne daga Sudan ta Kudu da yayin da Habasha ta bude kofarta ga 'yan Somaliya duk kuwa da irin kalubalen da ita kanta Habshar ke fuskanta ta bangaren abinci.