1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman hanyoyin magance cin zarafin mata

Suleiman Babayo
November 25, 2019

Gwamnatoci da dama daga kasashe masu karfin tattalin arziki zuwa masu tasowa na kara matakan magance matsalolin cin zarafin mata albarkacin ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yaki da cin zarafin mata.

https://p.dw.com/p/3TgOc
Bildergalerie Kenia Zwangsheirat Dezember 2014
Hoto: Reuters/S. Modola

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya kaddamar da gangamin magance hare-haren da ake kai wa mata sannan ya bukaci maza su sauya tunani. Gwamnati ta kara matakan ba sani ba sabo kan masu cin zarafin mata a cikin kasar baki daya. Kuma gwamnati ta yi alkawarin kara kasashe kudi domin magance kashe mata a gidaje da ake fuskata cikin kasra ta Afirka ta Kud.

Ita ma gwamnati Jamus ta ce alkaluman barazana da mata kimanin 114,000 suke fuskanta na cin zarafi a shekara na zama abu mai tayar da hankali a cewa Franziska Giffey ministar kula da iyali ta Jamus, wadda ta ce lamarin ya zama mai kada zuciya.

Haka gwamnatin Faransa ta bayyana shirin kara kashe kudi kan yaki da matsalolin cin zarafin mata da ake samu a kasar duk da yake tana sahun gaba a kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya.