1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin tsaro na kara kamari a Najeriya

Gazali Abdou Tasawa
February 20, 2020

A Najeriya matsalolin tsaro na kara kamari a yankunan da dama, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da yin tsayuwar gwamin jaki a game da bukatar 'yan majalisu da ma wasu 'yan kasar kan sauya hafsoshin soja.

https://p.dw.com/p/3Y5EJ
Nigeria | Niedergebrannte Fahrzeuge in Auno
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

A Najeriya matsalolin tsaro na kara kamari a yankunan da dama na kasar musamman na yankin arewacin kasar inda 'yan Boko Haram da kuma 'yan bindiga ke ci gaba da daukar rayukan jama'a. Sai dai kuma duk da kamari da yanayin tabarbarewar tsaron ke yi, gwamnatin kasar ta ce ba ta da niyyar sauya hafsoshin sojan kasar, wannan kuwa duk da kiraye-kirayen da wasu 'yan kasar da kuma musamman 'yan majalisa ke yi na ganin an sauya hafoshin tsaron kasar domin dora sabbin jini da za su fi tunkarar matsalolin na tsaro a fadin kasar.