1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin kafofin yada labaran Laberiya wajen yaki da rashawa

August 27, 2013

Gwamnatin Laberiya ta rufe gidan wata jarida bisa rahotonta a kan zargin gwamnati da rashawa.

https://p.dw.com/p/19XWa
Liberian President Ellen Johnson Sirleaf answers questions from journalists as she meets with members of the press at the Ministry of Foreign Affairs in Monrovia, Liberia Thursday, Nov. 10, 2011. Africa's first and only female president handily won re-election Thursday with 90.2 percent of the vote, but her victory has been rendered hollow and her government may struggle to prove its legitimacy because the opposition boycotted the poll. (Foto:Rebecca Blackwell/AP/dapd)
Hoto: dapd

A wannan Talatar ce hukumomin kasar Laberiya suka bayar da umarnin rufe gidan buga Jaridar "Frontpage Africa" da ke sahun farko a jerin jaridun kasar da suka yi fice. Daukar wannan matakin dai ya biyo bayan tsare shugaban jaridar, bisa zargin yi wa gwamnati kage a wani rahoton da ta buga game da cin hanci a cikin gwamnatin kasar. Dama tun a ranar Larabar da ta gabata ce, jami'an tsaro suka yi awon gaba da Rodney Sieh, babban darektan jaridar, bayan da kotun kolin kasar ta umarci jaridar ta biya tarar kudi dalar Amirka miliyan daya da dubu 600, domin buga labarin batanci a kan ministan harkokin noma a kasar J. Chris Toe.

Kotun kolin ta bayar da umarnin ci gaba da rufe gidan jaridar, har sai ta biya tarar baki daya. Wade Williams, daya daga cikin Editocin jaridar, ya shaida wa kanfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar, yini biyu kenan a jere, jaridar ba ta yin aiki, saboda jami'an tsaron da suka killace gidan bugata, domin yin aiki da umarnin kotun.

Tun dai a shekara ta 2009 ne, jaridar ta buga wani labarin da ya zargi ministan da sace kudin gwamnati, daga bisani kuma minista Toe ya gurfanar da ita a gaban kuliya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Mouhamadou Awal Balarabe