1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin Kerry kan matakin adawar Siriya

November 11, 2013

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya yi marhabin da shawarar da 'yan adawan Siriya suka yanke na shiga tattaunawar zaman lafiya, wanda ya kira babban ci-gaba.

https://p.dw.com/p/1AFYj
U.S. Secretary of State John Kerry speaks at a news conference with UAE Foreign Minister Abdullah bin Zayed Al Nahyan (not pictured) at the foreign ministry in Abu Dhabi, November 11, 2013. REUTERS/Jason Reed (UNITED ARAB EMIRATES - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya yaba matakin da 'yan adawan Siriya suka dauka na halartar taron wanzar da zaman lafiya da zai gudana a birnin Jeniva. A lokacin wata ziyarar aiki da ya ke yi a Hadaddiyar Daular Larabawa Kerry ya danganta wannan mataki da wani ci-gaba da mai ma'ana, a kokarin da ake yi wa kawo karshen rikcin da ya ki ci ya ki cinyewa a Siriya.

Su dai 'yan adawan na Siriya sun bukaci a sako daukacin fursunonin siyasa tare da bai wa kungiyoyi damar kai agaji a wuraren da ake gwabza fada, idan ana so su shiga a damasu a tattaunawar da za a a yi a kan makomar Siriya. Wannan dai shi ne karon farko da hadaddiyar jam'iyyun adawa ta nuna alamun cewa za ta halarcin taron na Jeniva.

Sai dai kuma masu kaifin kishin addini na wannan kasa sun riga sun yi fatali da goron gayyata da aka mika musu, inda suka ce ba za su tattauna ba matikar al-Assad na rike da madafun iko. Ba a dai bayyana lokacin da za a gudanar da taron ba, amma kuma bangaren shugaba Bashar al-assad ya riga ya bayar da tabbacin cewa zai tura da wakilai a birnin Jeniva.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinado Abdu-Waba