1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mauritius ce kan gaba a shugabanci na gari

October 3, 2016

Wani jadawali da gidauniyar nan ta Mo Ibrahim ta fidda na cewar kasar Mauritius ce ke kan gaba a nahiyar Afirka ta bangaren shugabanci na gari yayin da Somaliya ke zaman kasa ta karshe.

https://p.dw.com/p/2Qpjm
Mo-Ibrahim-Index für Regierungsführung in Afrika, 29.09.2014 in London
Hoto: Barefoot Live

Gidauniyar nan ta Mo Ibrahim da ke aiki kan shugabanci na gari a kasashen Afirka ta ce an samu cigaba ta fannin jagorantar kasashe a nahiyar ta Afirka a shekaru 10 da suka gabata. A wani jadawali da ta fidda, gidauniyar ta ce kasar Mauritius ce ke kan gaba yayin da Botswana da Cape Verde ke biya mata baya. Afirka ta Kudu da ke kan gaba wajen karfin masana'antu a nahiyar na kan matsayi na shidda yayin da Somaliya ke a matakin karshe.

Gidauniyar dai ta duba fannonin da suka danganci tsaro da kare hakkin dan Adam da tattalin arziki da kuma kiwon lafiya da cin hanci da sauran batutuwa gabannin fidda jadawalin. Bisa ga rahoto da aka fidda dai, rabin kasashen na Afirka sun samu koma baya a shekaru ukun da suka gabata ta bangaren tsaro da kuma kiyaye dokokin kasa.