1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mawuyacin halin yan gudun hijiran Afirka a Hamburg

August 14, 2013

Yan gudun hijira ma su tarin yawa daga Afirka cikin yan kananan kwale-kwale suna ci gaba kama hanya mai matukar wahala da hadari a tekuna domin neman isa nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/19PAh
Hoto: DW

A wannan Alhamis kawai, sai da aka ceto yan Afirka da yan gudun gudun hijira daga Syria da yawansu ya kai 500. Da yawa daga cikin su sukan kare wannan balaguro nasu ne a karkashin teku inda suke rasa rayukansu, kamar yadda aka rika samu tun daga yan makonnin baya. Ko da shike ziyarar da Paparoma Franziskus ya kai tsibirin Lampedusa na Italiya a farkon watan Yuli ta dauki hankalin duniya, amma ziyarar bata kawo wani canji ga yan gudun hijira a wannan tsibiri ba. Kasashen Turai da dama, cikinsu har da Jamus, suna ci gaba da nuna kyamar baiwa wadannan yan gudun hijira mafakar siyasa.

A rabin farko na wannan shekara, yan gudun hijira da suka shigo Jamus sun ninka akalla sau biyu. Sai dai kuma kasancewarsu a Jamus ba tana nufin kai tsaye zasu sami mafakar siyasar bane. Andreas daga kasar Ghana ya zama abin misali, saboda a bayan tafiya mai wahala cikin teku, da kyar shi da wasu yan Afirka da dama suka sami wurin zama a wani coci dake Hamburg.

Andreas dai ya dora fatansa gaba daya ne kan birnin Hamburg. Mutumin dan shekaru 30, ya sha tafiya mai tswo da sarkakiya kafin ya isa Hamburg. Bayan da ya kammala karatu a kasarsa ta asali wato Ghana, ya matsa zuwa Libya, domin neman kudi, inda yana can ne yakin da ya kawar da Muammar Gaddafi ya tashi, daga nan Andreas ya kara gaba, ya tsere ta cikin teku zuwa Turai, inda ya kare a Italiya. A can din ya zauna tsawon shekaru biyu a sansanonin yan gudun hijira dabam-dabam, kafin a bashi izinin zama, wato Visa na maziyarta.

"Yace sun zo sun tarad dani, suka ce ga Euro 400, amma zamu rufe duk wani shiri na taimako. Saboda haka ni da sauran wadanda muke tare tilas muka fice daga inda muke zaune karkashin shirin na taimako."

A Italiyan, Andreas tare da wasu yan guun hijira 80 aka basu dan kudi kalilan, aka kuma basu shawarar cewar su kama hanyar zuwa Jamus. Sun kuwa karbi wannan shawara, suka yi amfani da takardun Visa da suka samu suka iso Hamburg inda da farko suka rika kwana a kan tituna. A farkon watan Yuni, wani limamin kirista, Pastor Sieghard Wilm ya karbe su a cocinsa a yankin Sankt Pauli a birnin. Limamin Kiristan yace:

Obdachlose Flüchtlinge aus Afrika in Hamburg
Mafaka a wani coci dake birnin Hamburg....Hoto: DW

"Ba zai yiwu mu zura idanu muna ganin yadda mutane suke zaune cikin mummunan hali a kan tituna ba. Wadannan mutane ne ba dabbobi ba. Suna da bukatun su na yau da kullum, akwai kuma batun kare hakkin yan Adam, wadanda duka al'amura ne da tilas mu maida hankali kansu. Idan kuma yan siyasa suka ci gaba da rufe idanunsu, to mu kuwa tilas ne mu bude namu idanun. Haka dai al'amarin yake."

A halin yanzu, matakin da cocin ya dauka, ya kawo kace-nace tsakanin cocin da ya karbi yan gudun hijiran saboda tausaya masu da kuma hukumomin birnin Hamburg, dake nuni da dokar da tace duk dan gudun hijiran da ya shiga Italiya, to kuwa a can ne ya kamata ya nemi mafakar siyasa, saboda haka dokokin kungiyar hadin kan Turai suka tanadar. Kakakin majalisar mulkin Hamburg, Jörg Schmoll ya nunar da cewar:

"Wadannan mutane daga Afirka da suka zo mana, sun shigo ne da Visar maziyarta ta adadin tsawon watanni ukku. Bayan wannan lokaci basu da izinin ci gaba da zama a kasarmu, saboda haka tilas su koma inda suka fito."

Flüchtlinge Afrika Mittelmeer Boot Gefahr
....bayan tafiya mai matukar wahala cikin teku zuwa TuraiHoto: picture-alliance/dpa

Wannan matsala dai ta shafi yan gugun hijira akalla 300 ne da suka tsallako zuwa Turai daga Libya, wadanda zasu fuskanci barazanr sake mai da su da karfi zuwa Italiya.

Mawallafi:Erath/Umaru Aliyu
Edita: Saleh Umar Saleh