1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Kwango na da hannu a rikicin Kasai

Mouhamadou Awal Balarabe
June 20, 2017

Shugaban Hukumar Kare Hakkin bil Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad al-Hussein ya zargi gwamnati Jamhuriyar Kwango da ruruta wutar rikicin yankin kasai.

https://p.dw.com/p/2f1cW
Diplomat Zeid Ra'ad al-Hussein
Hoto: Reuters/P. Albouy

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi gwamnatin Kwango da marar hannu a wasu jerin hare-hare kan fararen hula a yankin kasai da ke tsakiyar kasar. A lokacin da yake bayani a birnin Geneva, shugaban Hukumar Kare Habbin dan Adam na Duniya Zeid Ra'ad Al Hussein ya nunar da cewar hukumomin Kwango na samar wa mayakan sa kai da makaman da suke aikata ta'asa da su.

Tun dai watan Staumban 2016 ne wasu magoya bayan wani basarake da aka kashe a yankin Kasai suka fara tayar da kayar baya da nufin daukar fansa. lamarin da haifar da fito na fito tsakanin 'yan tawaye da kuma sojojin gwamnati. Jami'ai uku da Majalisar Dinkin Duniya ta tura don gudanar da bincike sun rasa rayukansu a wannan rikici.

Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da cewar 'yan tawayen Kamwina Nsapu na sa yara aikin soje, yayin da gwamnati ke amfani da karfin fiye da kima. Wani rahoton da Malaman cocin Kwango suka fitar ya nunar da cewar mutane akalla dubu uku ne suka rasa rayukansu a rikicin na Kasai.