1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Myanmar ta kawo karshen kisan 'yan Rohingya

Gazali Abdou Tasawa
September 6, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga mahukuntan kasar Bama ko Myanmar da su gaggauta daukar matakan kawo karshen kisan da ake yi wa musulmi marasa rinjaye 'yan kabilas Rohingya.

https://p.dw.com/p/2jQnV
Palästina Guterres im Gaza-Streifen
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio GutteresHoto: Reuters/M. Salem

Wannan kiran na Majalisar Dinkin Duiniya na zuwa ne lokacin da dubban 'yan Kabilar ta Rohingya ke ci gaba da tserewa zuwa makwabciyar kasar Bangaladash. Sai dai kuma Shugabar gwamnatin kasar ta Bama Aung San Suu Kyi ta musanta zargin da ake na aikata kisan kiyashi kan 'yan kabilar ta Rohingya, tana mai zargin kafofin yada labarai da ruruta wutar rikicin. Kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun bayyana cewa daga ranar 25 ga watan Agusta, lokacin da rikicin baya-bayan nan ya barke a cikin jihar Rakhine da ke arewa maso yammacin kasar. Ya zuwa yanzu dai bayanai na cewa kimanin 'yan kabilar ta Rohingya dubu 125 ne suka tsere zuwa kasar Bangaladash, kyayin da wasu da dama ke kan hanya.

Rohingya in Myanmar und Bangladesch
Wasu 'yan Rohingya da ke tserewa rikiciHoto: picture-alliance/dpa/M.Alam

Akasarin mutanen na tserewa ne ayari ayari na iyalai da suka kunshi tsofaffi da yara da mata, inda bayan doguwar tafiya a kasa suke isa gabar ruwa inda daga nan suke amfani da kwale-kwale marasa inganci wajen ketarawa zuwa kasar ta Bangaladash inda da dama ke mutuwa cikin ruwa.

A halin yanzu dai dubban 'yan kabilar ta Rohingya, na jibge a sansanonin 'yan gudun hijira daban-daban da aka tanada a harabobin makarantun kasar ta Bengladesh inda kungiyoyin agaji suka ce mutanen na rayuwa cikin kuncin karancin abinci da ruwan sha, kana da dama daga cikinsu na fama da rashin lafiya da kuma rauni a jikinsu.

A cikn wannan yanayi ne dai babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi kira ga mahukuntan kasar ta Myanmar da su gaggauta daukar matakan dakatar da wannan rikici.  "Ya ce, ina kira ga dukkanin shugabannin kasar Myanmar na Soji da farar hula, da su gaggauta kawo karshen wannan tashin hankali wanda ka iya haifar da da babban rikici a yankin baki daya"

Shi ma asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce kananan yara dubu 28 ne rikicin ya rutsa da su a jihar ta Rakhine ba tare da an iya shiga an ceto su ko kai masu dauki ba. Akan haka ne babban jagoran na Majalisar Dinkin Duniya Anthonio Guterres ya sanar da soma nazarin hanyoyin samarwa da 'yan kabilar ta Rohingyas 'yanci a jihar ta Rakhine.