1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta amince da tsagaita wuta a Siriya

Abdullahi Tanko Bala
February 24, 2018

Wakilai a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya sun kada kuri'ar amincewa da tsagaita wuta a Siriya na kwanaki 30 ba tare da jinkiri ba.

https://p.dw.com/p/2tHqv
USA Sicherheitsrat der Vereinten Nationen Friedensverhandlungen in Kolumbien
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Rajmil

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar goyon bayan tsagaita wuta a Siriya na tsawon kwanaki 30 domin bada damar kai taimakon jin kai ga al'umma.

Da farko dai Rasha wadda ke mara baya ga shugaba Bashar al Asad ta yi barazanar hawa kujerar naki amma daga bisani dukkan wakilan kwamitin sulhun su 15 suka amince da kudirin tsagaita wutar ba tare da wani jinkiri ba.

Kasashen Kuwait da Sweden sune suka gabatar da daftarin kudirin a ranar Laraba yayin da  a waje guda shi ma sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kiran dakatar da fada a yankin.

Amincewa da kudirin dai na zuwa ne yayin da jiragen yaki ke luguden bama bamai a gabashin Ghouta gari na karshe dake hannun yan tawaye.