1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Idlib ya tagayyara dubban jama'a

Abdullahi Tanko Bala
February 14, 2020

Mummunan musayar wuta tsakanin sojojin gwamnatin Siriya da ke samun goyon bayan Rasha da kuma mayakan yan tawaye da Turkiya ke marawa baya na cigaba da haifar da mummunan halin tagaioyarar al'umma.

https://p.dw.com/p/3XlCB
Syrien Idlib Flüchtlingslager
Hoto: picture-alliance/AA/E. Turkoglu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yan Syria fiye da dubu 140 aka tagaiyara cikin kwanaki a yakin da ke cigaba da gudana a Idlib wanda ya kaswo adadin mutanen da suka tagaiyara zuwa dubu dari takwas.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce kashi 60 cikin dari na mutanen dubu 800 da aka tagaiyara a watan Disambar bara yara ne kanana.

A nasa bangaren Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas yace wajibi ne a kawo karshen hare haren da ke gudana a Idlib. Ya bukaci samo hanya ta masala domin warware rikicin.