1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi Allah wadai da cin zarafin mata a Kwango

October 15, 2010

MDD ta ce tilas ne a dauki matakan gaugawa akan fyade da kisa da sojojin Kwango suke yi akan al'uma

https://p.dw.com/p/Pegu
Margot WallströmHoto: picture-alliance/dpa

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a yankin gabacin Afirka da ke kula da yaki da cin zarafin Mata Margot wallstrom

ta bayyana fargabanta dangane da yadda sojojin gwamnatin ke ci- gaba da aiwatar da fyade da kuma kisa akan mata galibi yara kanana a gabacin Kwango.

Margot wacce ke magana a gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin duniya. Ta yi gargadin cewa a kwai bukatar daukar matakai na gaugawa ga al'uma yankin wanda daman suka fuskanci lamarin fyade daga sojojin kasar Ruwanda da na 'yan tawayyen Mai Mai a cikin watan yuli da ya gabata.

Mawallafi:Abdurahaman Hassane

Edita :Abdullahi Tanko Bala