1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abin da ke jawo Habo

Yusuf BalaOctober 14, 2015

Alamu ne na wata cuta a jikin dan Adam alal misali cutar Hawan Jini a cewar Dakta Kabir Alfunduki na cibiyar nazarin cutittika da ke da alaka da koda ta Abubakar Imam Eurology Center Kano.

https://p.dw.com/p/1GoYZ
Afrikaner in einem Labor mit Mikroskop
Hoto: Fotolia/gwimages

Yusuf Bala: Me tambaya na son ya sani ko Habo cuta ce?

Dakta Kabir Alfundiki: Shi Habo wato jini da ke fita ta hancin dan Adam ba ciwo ba ne mai zaman kansa, amma zai iya kasancewa alamu ne na wata cuta alal misali idan Hawan Jini idan ya yi yawa a jikin dan Adam mutum na iya yin Habo.

A wasu lokutan kuma amfani da wasu magunguna su wuce kima na iya kawo Habo alal misali Aspirin, Wani lokaci kuma akwai ciwon da ake haifar mutum da shi musamman a kananan yara, kawai sai su tashi da safe daga bacci sai su gani sun zubar da jini da yawa ta hancinsu.

Yusuf Bala: To likita baya ga Aspirin wane magani ke kawo Habo?

Dakta Kabir Alfundiki: Akwai nauin magungunada dama da kan tsinka jini, su ma ba koda yaushe sukan jawo Habon ba, idan amfanin ne ya wuce kima musamman shi Aspirin din wanda mutane kan yi amfani da shi da yawa har ya wuce ka'idar likita.

Yusuf Bala: Shin akwai wasu matakai da mutumin da ke fama da Habo zai iya dauka ko kuwa.

Dakta Kabir Alfundiki: A gaskiya abu ne na gaggawa da ake bukatar mutum ya je ganin likita musamman idan mutum yana yin Habo akai-akai, kuma likitan da ya kamata ya je ya gani shi ne likitan da ke zama kwararre a fannin makogwaro da hanci da kunne.