1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel: Ba gaba tsakanin Jamus da Amirka

Abdul-raheem Hassan
July 20, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus ta ce babu matsananciyar alaka tsakaninta da Trump, amma ta nuna shakku kan yadda batun 'yan gudun hijira ya rage tasirin jam'iyyun kawance da ke mulki.

https://p.dw.com/p/31pBl
Sommerpressekonferenz Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ambata hakan ne yayin amsa tambayoyin manema labaru gabannin fara hutunta na bazara a wannan shekarar, inda ta ce ya zama wajibi su yi tsayin daka wajen dawo da martabarsu bayan rikicin 'yan gudun hijira.

Sai dai Merkel ta kuma jaddada matsayin Jamus game da dangantakarta da Amirka, inda ta ke cewar ba gaba tsakanin kasashen biyu, amma ta zargi shugaba Donald Trump da lalata huldar kasuwaci tsakanin Amirka da Jamus, inda ta ce: "Ina ganin abin da muka saba ne aiki cikin zafin kai, ko da yake dangantakar kasuwanci tsakaninmu da Amirka na da muhimmanci sosai. Amma alkiblar siyasata baya wuce yin aiki tare domin samun nasara baki daya."