1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel: Kyamar baki guba ce

February 20, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce matsalar wariyar launin fata tsakanin al'uma wata guba ce mai muni. Ta fadi hakan ne a martaninta kan hare-hare na garin Hanau.

https://p.dw.com/p/3Y45y
Deutschland Berlin | Statement Angela Merkel, Bundeskanzlerin | Hanau Schießerei
Hoto: Getty Images/S. Gallup

Shugabar gwamnatin Jamus ta jajanta wa iyalan mutane tara da suka mutu sakamakon hare-hare biyu da aka kai kan wasu shagunan sayar da tabar shisha a wajen birnin Frankfurt cikin daren da ya gabata.

Angela Merkel wadda ta bayyana hare-haren na garin Hanau a matsayin na kyamar baki, ta ce matsalar wariyar launin fata tsakanin al'uma wata guba ce mai muni.

Ta ce ana yin dukkanin mai yiwuwa don gano tushen kashe-kashen mara dadi. Kuma bincike ya gano wanda ya aikata su ya yi su ne da niyyar nan da wasu ke da ita ta kyamar baki walau saboda addininsu ko kuma launin fata.

A jawabin da ta yi nan a Berlin, Angela Merkel ta fada cikin kakkausar lafazi, cewar Jamus na kan matsayinta na girmama duk wani da ke a kasar koda kuwa daga ina ne tushensa yake.

Tuni dai jami'an 'yan sandan Jamus suka bayyana mutuwar mutumin da ake zargi da aikata danyen aiki.