1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta buƙaci ƙafa tsauraran dokoki ga cibiyoyin kuɗi a Turai.

May 20, 2010

Jamus ta bayyana samar da sabbin dokoki a matsayin mafita ga rikicin tattalin arziƙi a Turai

https://p.dw.com/p/NSoJ
Hoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fara yunƙurin yin matsin lamba ga samar da tsauraran ƙa'idoji da kuma haraji a ɓangaren kasuwanin hada hadar kuɗi. A lokacin da take yin jawabi a wajen babban taron samar da dokoki a sashen kuɗin dake gudana a birnin Berlin, fadar gwamnatin Jamus, shugabar gwamnatin ta ce, tilas ne a samar da sabbin dokokin da zasu zama zakarar gwajin dafi a tsakanin ƙasashen Turai.

Hakanan ta bayyana ƙudurin gabatar da batun samar da dokokin a lokacin taron manyan ƙasashen 20 dake da ƙarfin tattalin arziƙi a duniya na G20n da ƙasar Canada za ta karɓi baƙuncin sa a watan gobe - Idan Allah ya kaimu. Merkel ta kuma mayar da martani ga wasu ƙasashen da ke ganin faɗuwar martabar takardun Euro ba damuwar su ba ce:

" Idan har wasu ƙasashe ukku za su ce wannan abin bai shafe su ba, to, kuwa wannan wata babbar koma baya ce. Roƙona shi ne, mu haɗa kai waje guda domin samar da wata alamar ƙarfin da muke da shi a lokacin taron G20."

Sai dai kuma ministar kula da harkokin tattalin arziƙin Faransa Christine Lagarde, tana da ra'ayin daya sha banban dana Merkel, inda ta furta cewar, babu wani hatsarin da takardun kuɗin ke fusksanta.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu