1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na cikin hali na gwajin karfinta a matsayin dunkulalliya

Mohammad Nasiru AwalFebruary 17, 2016

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi gargadi da a guji bin abinda ta kira gurguwar alkibla dangane da matsalar 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/1Hx0v
Deutschland Regierungserklärung Angela Merkel im Bundestag
Hoto: A. Berry/AFP/Getty Images

Kwana guda gabanin taron kolin kungiyar tarayyar Turai EU, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi gargadi da a guji bin abinda ta kira gurguwar alkibla dangane da matsalar 'yan gudun hijira. A lokacin da take jawabi gaban majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, Merkel ta ce dole EU ta yi duk iya kokarin gano bakin zaren magance matsalolin ta yadda ba za su yi wa Turai da kasashen membobin EU illa ba. Ta ce dole ne kasashen Turai sun yanke wa kansu shawara irin alkiblar da za su fuskanta.

"A lokaci daya kuma wajibi ne mu nuna cewa kungiyar tarayyar Turai na da karfin da za ta iya fuskantar babban kalubalen wannan zamani tare kuma da gano hanyoyin magance su."

Da ta juya kan rikicin Siriya kuma Merkel ta yi kira da a bude wani yankin tudun mun tsira ga fararen hula da yakin ya rutsa da su.

"Zai taimaka idan aka samar da wannan yanki a Siriya inda za a haramta wa bangarorin da ke yaki a kasar yin shawagi ko kai harin bam suna kashe fararen hula."

A ranakun Alhamis da Jumma'a shugabannin EU za su yi wani taron koli daidai lokacin da ake samun baraka tsakaninsu kan yadda za a tinkarin batun 'yan gudun hijira.