1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta fuskanci koma baya na siyasa

July 18, 2010

Murabus na magajin garin Hamburg ka iya janyo cikas ga Merkel

https://p.dw.com/p/OOUX
Magajin garin Hamburg, Ole von Beust a lokacin da yake ba da sanarwar murabus ɗinsa.Hoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta sake fuskantar raguwar magoya  bayanta  sakamakon murabus na magajin garin Hamburg, Ole von Beust. Birnin Hamburg da ke zaman na biyu mafi girma a  Jamus na ɗaya daga cikin jihohin ƙasar guda 16. Von Beust kamar dai Merkel mamba ne na jam'iyyar CDU da ya shafe shekaru kusan tara yana mulkin jihar ta Hamburg. Ya faɗa wa manema labarai cewa zai sauka daga muƙaminsa a ranar 25 ga wata mai zuwa, yana mai kafa dalilai na gaban kansa. Kenan shi ne na shidan shugabannin jihohi na jam'iyyar CDU da suka bar muƙamansu cikin watanni goma da suka gabata.  Kafafen yaɗa labaran Jamus sun kira murabus ɗin na von Beust tamkar babban koma baya ga Merkel.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Mohammad Nasiru Awal