1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bitar yarjejeniyar G20 da Afirka a Berlin

Abdul-raheem Hassan
November 19, 2019

Shugabannin kasashen Afirka za su gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da sauran kusoshin gwamnati da 'yan kasuwa a birnin Berlin domin yin waiwaye kan tasirin yarjejeniyar habaka tattalin arzikin Afirka.

https://p.dw.com/p/3THWs
Compact with Africa Afrikagipfel Bundesregierung Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da wasu shugabannin AfirkaHoto: picture-alliance/dpa/A. Hilse

Manufar taron shi ne maida hankali kan yadda za a jawo hankalin masu hannu da shuni daga kasashen masu arziki domin zuba jari a nahiyar Afirka.

Shekaru uku kenan da gwamnatin Jamus ta kirkiro da tsarin kulla yarjejeniyar kawancen bunkawa tattalin arzikin kasashen Afirka "Compact with Afrika" inda ma'aikatar raya kasashe na Jamus ta fara yarjejeniyar da kasashen Tunisia da Ghana da Ivory Coast.

A shekarar 2019 ministan raya kasashe masu tasowa na Jamus Gerd Müller zai rattaba hannu kan sabuwar yarjejniya da kasashen Moroko da Senegal da kuma Habasha.