1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mexiko da Turai za su sabunta yarjejeniyar kasuwanci

Suleiman BabayoJune 12, 2015

Kungiyar kasashen Turai da Mexiko za su tattauna kan sake sabunta yarjejeniyar kasawanci tsakani zuwa ta zamani

https://p.dw.com/p/1FgNn
Brüssel Pena Nieto EU-Mexico Gipfel Juncker und Tusk
Hoto: Getty Images/AFP/E. Dunand

Kasar Mexiko da kungiyar kasashen Tarayyar Turai sun amince da kaddamar da tataunawa kan kulla sabuwar yarjejeniyar cinikayya tsakanin bangarorin biyu.

Shugaba Enrique Pena Nieto na kasar ta Mexiko ya bayyana haka wa manema labarai a birnin Brussels na kasar Beljiyam, inda ya nunar da mahimmancin haka saboda yadda Amirka da Kanada suka zama manyan masu hulda da kasar. Sabon matakin zai taimaka wa Mexiko ta shiga jerin kasashen da suka sabunta yarjejeniya ta zamani da kasashen Tarayyar Turai.