Michel Djotodia ne sabon shugaban Seleka
July 12, 2014Kungiyar 'yan tawayen Seleka na Jamhuriyar Afirka ta TSakiya ta sake bayyana tsohon shugaban kasar Michel Djotodia da ya dare kan karagar mulki bayan da ya jagoranci kungiyar ta samu nasarar kifar da gwamnatin Francois Bozize a matsayin shugabanta.
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar ta ma sake nada wasu daga cikin tsoffin shugabanninta a matsayin shugwabanninta na yanzu a yayin babban taron da ta gudanar. Rikicin addini dai ya barke a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar tun bayan da Djotodia ya dare kan karagar mulki wanda hakan ne kuma ya tilasta masa sauka daga karagar mulkin a watan Janairun da ya gabata.
A yanzu haka dai dubun dubatar 'yan Jamhuriyar Afirka dta Tsakiyarne aka tilastawa kauracewa gidajensu yayin da wasu daruruwa suka hallaka sakamakon kisan da 'yan kungiyar tawayen Anti-Balaka ta Kiristocin kasar kewa Musulmi.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe