1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harkokin wajan Birtaniya ya sauka birnin Teheran

Salissou BoukariAugust 23, 2015

A wannan Lahadin ce Birtaniya ta buda ofishin jakadancinta aTeheran babban birnin kasar Iran, yayin da ita kuma Iran ta buda nata ofishin jakadancin a fadar gwamnatin Birtaniya da ke birnin London.

https://p.dw.com/p/1GK8j
Hoto: Reuters/D. Staples

Wata sanarwa ta ofishin ministan harkokin wajan kasar ta Birtaniya ta ce a wannan Lahadin ce Hammond, Ministan harkokin wajan kasar yake soma wata ziyara ta kwanaki biyu a kasar Iran domin buda ofishin jakadancin na su, bayan da aka rufe shi shekaru hudu da suka gabata. Wannan dai ita ce ziyara ta farko ta wani shugaban diflomasiyyar kasar Britaniya a Iran tun shekara ta 2003, kuma wannan ziyara na zuwa ne bayan ta ministocin Turai da dama da suka ziyarci kasar ta Iran, sakamakon cimma yarjejeniyar da aka yi a ran 14 ga watan Yuli tsakanin Iran din da manyan kasashen duniya shida.