Ministan raya kasa na Jamus na ci gaba da ziyara a Najeriya
June 12, 2014Ministan kula da ayyukan raya kasa na tarayyar Jamus Gerd Müller yana Abuja babban birinin tarayyar Najeriya a ci gaba da ziyarar aikin da yake kai wa wannan kasa. A taron manema labaran da yayi dazun nan a Abuja ministan ya zayyana jerin ayyukan hadin kai guda hudu da Jamus da Najeriya za su fi mayar da hankali kansu, inda ya ce: "Za mu karfafa hadin guiwa a bangarorin ilimi musamman ga yara mata da koyon sana'o'i da binciken kimiyya a fannin samar da isasshen abinci a cikin kasa, za mu kuma kara ba da tallafi a bangaren kare hakkin mata da kuma 'yan mata."
Ziyarar minister Müller ta zo ne a daidai lokacin da hare-haren kungiyar Boko Haram suka karu a Najeriya. An dai shirya tattaunawa tsakaninshi da shugaba Goodluck Jonathan da shugaban hukumar kungiyar ECOWAS Kadre Desire Ouadraogo da kuma masu fafatukar neman ceto 'yan matan Chibok na "Bring back our girls". A ranar Laraba ministan ya kai ziyara jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu