1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministocin Sunni sun yi murabus daga gwamnatin Irak

August 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuF3

Ministoci 6 yan sunni ,sunyi murabus daga gwamnatin Irak.

Sun yanke wannan shawara, a sakamakon wani taron manema labarai da su ka shirya, ɗazunan nan a birnin Bagadaza.

Tun ranar 16 ga watan da ya gabata su ka bayyana aniyar yin murabus daga muƙaman su, muddun gwamnati bata tsaida abunda su ka kira ba, durra mikiya, da kuma kame -kamen barkatai, da sojjojin gwamnati da na Amurika ke ci gaba da yi wa yan ɗarikar Sunni.

A cewar masharanta, ko shakka babu, wannan murabus, zai ƙara maida hannun agogo baya, ga yunƙurin samar da zaman lahia a ƙasar Irak.

A game halin da ake ciki a ƙasar Irak ,a ƙalla mutane 1.700 su ka rasa rayuka, a tsawan watan da ya gabata.

Hare-hare sun ƙara tsamari a watan Juli a fadin ƙasar baki ɗaya, duk kuwa da matakan tsaro tsatsaura, da sojojin Amurika da na Irak su ka ɗauka.

A yau kuma kussan mutane 70 su ka kwanta dama, cikin wasu sabin hare-haren ta´adanci.

A nata ɓangare, Amurika ya zuwa yanzu, ta yi asara sojoji 3.653.