1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mnangagwa ya hau karagar mulki

Ramatu Garba Baba
November 24, 2017

A wannan makon yawancin jaridun na Jamus sun rubuta sharhinsu ne akan kasar Zimbabuwe bayan da mulkin Robert Mugabe na sama da shekaru Talatin ya zama tarihi.

https://p.dw.com/p/2oC26
Simbabwe Harare Vereidigung Präsident Emmerson Mnangagwa
Hoto: Reuters/M. Hutchings

Jaridar Süddeutsche Zeitung a sharhinta mai taken 'Kada ya karbi mulki' ta ce bayan murabus din shugaba Robert Mugabe sakamakon matsin lamba daga jam'iyyarsa ta ZANU-PF da kuma sojoji, ta bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Emmerson Mnangagwa wanda ya fice daga kasar bayan da Mugabe ya kore shi a wani mataki da ake kallo na sharewa matarsa Grace Mugabe hanya domin ta gaje shi zai dawo Zimbabuwe bisa amincewar jam'iyyar ta ZANU-PF  domin karbar ragamar iko. Al'amura sun rika tafiya cikin sauri inda shugaban majalisar dokoki Jacob Mudenda ya sanarwa zauren majalisar a birnin Harare cewa ya sami takarda daga jam'iyyar ZANU-PF cewa ta nada Emmerson Mnangagwa domin ya gaji Mugabe mai shekaru 93 a matsayin shugaban riko zuwa lokacin da za'a gudanar da zabe.

Simbabwe Harare Vereidigung Präsident Mnangagwa
Alkalai da suka halaci bikin rantsar da shugaban kasaHoto: picture-alliance/AP Photo/C. Torchia

Jaridar ta ce Mnangagwa ba bako bane a siyasar Zimbabuwe. Da shi aka yi damawa a mulkin  kama karya na Mugabe tun bayan samun mulkin kai inda ya zama dan gaban goshin Mugabe tare da rike mukamin shugaban hukumar leken asiri da kuma minista shari'a. Kungiyoyin kare hakkin dan Adam na  kallonsa a matsayin daya daga cikin wadanda ke da alhakin kisan gilla da aka yiwa al'umma a yankin Matabeleland da ya yi sanadiyar mutuwar dubban jama'a a shekarun 1980. Saboda halayyarsa ta ba sani ba sabo da ya sa ake masa lakabi da Kada.Jaridar ta Süddeutsche Zeitung ta ce a yanzu gagarumin aiki da ke gaban Mnangagwa shi ne tunkarar kalubalen siyasa da na tattalin arziki da suka dabaibaye kasar. Sai dai Madugun adawa Morgan Tsvangirai ya bukaci a gudanar da zabe na gaskiya da adalci ba tare da jinkiri ba.

Jaridar Frankfurter Alkgemeine Zeitung a nata sharhin, tsokaci ta yi tare da jirwaye mai kamar wanka inda ta ce tuni Mugabe ya ja baya kafin jama'a su yanke masa kauna. Ala ayya halin dai sakamako biyu ne ke tattare da 'yan siyasa. Ko dai kimar ka da martabarka su dore a rika tunawa da kai tsawon lokaci ko kuma faduwar daraja kasa wanwar. Jaridar ta ce daga cikin 'yan mazan jiya da suka yi wa Zimbabuwe gwagwarmaya wadanda suka hada da Joshua Nkomo da Pastor Ndabaningi Sithole da kuma Bishop Abel Muzorewa, Mugabe ya yi faduwar bakar tasa inda jama'ar Zimbabuwe a ciki da wajen kasar ke murna da sowa da kawo karshen mulkinsa na kama karya.

Simbabwe Harare Robert Mugabe
Mulkin Robert Mugabe ya zama tarihiHoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

Ita kuwa jaridar Der Spiegel a sharhinta mai taken wanene zai biyo bayan Mugabe? Ta ce a yanzu dai ta faru ta kare wai an yiwa mai dami daya sata. Bayan gwagwarmaya tsakanin shugaban na kama karya da iyalinsa da kuma sojoji, shin sauyi ne na dimokradiyya aka samu ko kuma wani salon kama karyar za'a shiga? Jaridar ta ce a karshen tirka tirkai dai Mnangagwa mai shekaru 75 da ake yi wa lakabi da Kada shi ya yi nasarar cin gadon mulki. A yanzu zai jagoranci kasar zuwa zabe na gaba da za'a yi a shekara mai zuwa. Mnangagwa ya tsara aukuwar hakan daga nesa. Shugaban hafsan sojin kasar a cewar jaridar Der Spiegel ya je kasar Chaina babbar aminiyar Zimbabuwen. Kuma majiyoyi na diplomasiyya na cewa Beijin ta bada sahalewa ga daukar matakin kawar da Mugabe idan za a yi shi yadda ba za'a ga kamar an yi masa juyin mulki ba. Yanzu dai mulkin Mugabe a Zimbabuwe ya zama tarihi.