1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MONUSCO na shiga tsakani a rikicin Kwango

Gazali Abdou Tasawa
April 19, 2017

Majalisar ministocin Kwango ta kasa samuwa sabili da sabani tsakanin 'yan adawa da bangaren gwamnati. A kan haka ne rundunar zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta MONUSCO ta sanar da shiga tsakanin bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/2bV0Y
Demokratische republik Kongo UN Friedensmission Monusco
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

A ranar bakwai ga watan Afirilu 2017 ne Shugaba Kabila ya nada Bruno Tshibala  wanda ya yi tawaye daga babbar jam'iyyar adawa ta UDPS ta marigayi Etienne Tshisekedi a matsayin sabon Firaministan kasar. Matakin da jam'iyyar ta UDPS ta kalubalanta ta na mai cewa ya sabawa yarjejeniyar 31 ga watan Disamba 2016 da ta tanadi mika mukamin shugaban gwamnati ga 'yan adawa. Lamarin da ya haifar da cikas wajen kafa sabuwar majalisar ministoci a kasar ta Kwango.

Sai dai bayan da ya amince a bisa manufa da nadin sabon Firaminista, jagoran rundunar zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Demokaradiyyar kwango ta Monusco Mamane Sambo Sadikou ya gana da bangarorin siyasar kasar, inda ya yi masu tayin shiga tsakani ta yadda za su kai ga yin sulhu. Tayin da babbar jam'iyyar adawar ta UDPS ta karba. Sai dai a cewar Augustin Kabuya kakakin wannan jam'iyya duk wani sulhu da ake neman cimma zai wuya matsawar ba a mika wa jam'iyyarsa ta UDPS mukamin Firaminista ba:  

Étienne Tshisekedi
Bayan rasuwar Étienne Tshisekedi ne rikici ya dada dagulewa a KwangoHoto: picture-alliance/dpa/T. Roge

Ya ce " sura ta uku ta yarjejeniyar da muka cimma ta ce jam'iyyar adawa ta UDPS ta bada sunan mutunen da za a nada Firamnista. To amma ba ita ta mika sunan Tsibala ba. Don haka mu ba wa shugaba Kabila kai bori ya hau ba kamar dai wani halittacen shugaba. Mu a wurinmu ta keta haddin yarjejeniyar, don haka muke kira gareshi da ya mutuntata kawai"

Kungiyar Limaman Kiristocin kasar ta CENCO ta gana da shugaban rundunar Monusco, inda Mamane Sambo Sadikou ya yi mata bayani kan tattaunawar da ya yi da bangarorin siyasar kasar, da bukatar ganin ta shigo a cikin shirin neman sasanta rikicin siyasar. Sai dai abin tambaya a nan shi ne a bisa wani sharadi ne kungiyar limaman Kiristocin ta amince ta karbi wannan tayi bayan ficewar da ta yi a baya daga ciki. Donatien Nshole shi ne mataimakin magatakardan kungiyar Kiristocin DRC din ta CENCO .

Ya ce " tunda har bayan tattaunawa da jam'iyyar adawa ta UPS ne shugaban kasa ya nada sabon Firaminista, muna ganin wani ci gaba ne da ya kamata an yi amfani da shi a mance da wasu rigingimu na jiji da kai. Kungiyar CENCO ba zata koma baya ba ga sake tuntubar bangarorin daya bayan daya ba"    

Kongo Bischöfe geben Vermittlerrolle auf
Limaman Kiristoci sun taimaka wajen kwantar da kurar rikicin siyasar KwangoHoto: Getty Images/AFP/J. D. Kannah

 Sai dai da DW ta tuntubimMinistan cikin gidan kasar ta Jamhuriyar Kwango Ramazani Shadary ta wayar tarho kan wannan batu, ya ce  sun karbi tayin Majalisar Dinkin Duniya amma dai kuma a game da batu nadin Firamnista bakin alkalami ya rigaya ya bushe. ya abin da ke nuni da cewa ga bisa dukkan alamu tsugunne tashi ba ta kare ba a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango.