1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moroko na son komawa cikin kungiyar AU

Salissou Boukari
December 1, 2016

Gwamnatin kasar Moroko ta zargi shugabar Hukumar Tarayyar Afirka kuma Nkosazana Dlamini-Zuma da yunkurin tare mata hanya a kokarin da take na komawa a cikin kungiyar ta Tarayar Afirka.

https://p.dw.com/p/2TbUS
König Mohammed VI
Sarkin Moroko Mohammed na VIHoto: imago/CTK Photo

A tsakiyar watan Yulin da ya gabata ne dai, Sarki Mohammed na VI na Moroko ya yi fatan ganin kasarsa ta koma cikin gaggawa ga babban gida na Tarayyar Afirka, wanda ta bari tun daga shekara ta 1984 domin nuna adawarta da amincewa da yankin Yammacin kasar  a matsayin kasa mai cikakken 'yanici, wato Jamhuriyar Demokaradiyyar Saharawi. Wannan sanarwa dai da ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Morokko ya fitar, ta ce ko a watan Satumban da ya gbata ma, shugabar  Hukumar ta Tarayyar Afirkan Dlamini-Zuma ta jinkirta batun shigar da bukatar kasar ta Morokko ta komawa cikin kungiyar ta Tarayyar Afirka, inda ta kirkiro da wasu sababbin sharudda wanda hakan ya sa ta yi watsi da wasikun goyon bayan kasar ta Moroko da kasashe mambobin kungiyar suka aiko, abin da kasar ta Moroko ta ce yin hakan tamkar nuna bangaranci ne daga shugabar Hukumar ta Tarayyar Afirka. Kasar ta Morokko dai  za ta iya komawa cikin kungiyar ta Tarayyar Afrika, amma sai kashi biyu cikin uku na kasashe mambobin kungiyar sun kada kuri'ar amincewarsu kwatankwacin kasashe 36 kenan, wanda ake ganin wannan batu ya buda wata fafatawa ta karkashin kasa tsakanin kasashen Moroko da Aljeriya wajen shawo kan kasashen da za su kada kuri'unsu wanda zai wakana a zaman taron kungiyar na farkon shekara mai kamawa ta 2017 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha da ke a matsayin cibiyar kungiyar, kana tuni ta mallaki takardun amincewa na mafi yawan kasashe mambobin kungiyar masu goyon bayan komawarta da ta kira babban gidanta na gado.