1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moroko ta koma Tarayyar Afirka

January 31, 2017

Taron shugabannin kasashen Afirka da ya gudana a birnin Addis Ababa na Habasha ya dauki matakan da suka hada da sake mayar da Mokoro cikin kungiyar da gami da zaben sabon shugaban hukumar gudanarwa na kungiyar.

https://p.dw.com/p/2WjRt
Äthiopien Mohammed VI König von Marokko
Hoto: Getty Images/AFP/Z. Abubeker

Tarayyar Afirka ta karkare taronta da amicewa kasar Moroko sake hadewa kungiyar a matsayin wakiliya, taron ya kuma bukaci hadin guiwa na dinke matsalolin da addabar kasashen da ke nahiyar baki daya.

Äthiopien Mohammed VI König von Marokko
Hoto: Getty Images/AFP/Z. Abubeker

Taron na yini biyu, da ya hada kan wakilan kasashe mambobin Tarayyar Afirka a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, ya karkare da batutuwa masu daukar hankali. Bai wa kasar Moroko damar sake hadewa da Tarayyar Afirka, na cikin batutuwan da ya cimma tasiri. 

Afrikanische Union Marokko nach 33 Jahren wieder aufgenommen
Hoto: picture alliance/AA/Minasse Wondimu Hailu

Mambobin kungiyar 39 cikin 54 suka rattaba hannu kan amincewa Moroko ta sake dawowa bayan ballewar ta shekaru 33 baya. A baya dai Moroko ta ɗauki yankin Yammacin Sahara a matsayin wani ɓangare na ƙasarta mai cin gashin ganta kamin ta yi hannun riga da tsohuwar kungiyar haɗa kan Afirka (OAU) a shekara ta 1984. Kuma karkashin sabon tsarin Moroko ta amince da bai wa  Yammacin Sahara 'yanci kafin aka yarda ta dawo kungiyar ta Tarayyar Afirka. To sai dai a gefe guda, taron ya cimma nasara kan zaben ministan harkokin wajen kasar Chadi Moussa Faki a matsayin shugaban hukumar gudanarwa ta Tarayyar Afirkar, a matsayin wanda ya gaji Nkosazana Dlamini-Zuma daga Afirka ta Kudu.